Alwassiyya Channel Nigeria

Alwassiyya Channel Nigeria

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Alwassiyya Channel Nigeria, Government House Road, Abuja.

02/08/2026

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah Ya yi wa fitaccen mawakin siyasa Muhammad Kosan Waka rasuwa bayan ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya.

Rasuwar tasa ta girgiza masoya da abokan sana'arsa tare da al'ummar da s**a san shi, inda ake ci gaba da bayyana alhini da addu'o'i a gare shi.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata kabarinsa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya ba iyalansa, 'yan'uwansa da daukacin masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.

01/08/2026
31/07/2026

USTAZ SANUSI ASADUS SUNNAH AMORE YA YI ADDU'AR FATAN ALKHAIRI GA SHEIKH ISAH ALI IBRAHIM PANTAMI

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Sakkwato, Ustaz Sanusi Asadussunnah Amore, ya yi addu'ar fatan alkhairi ga Sheikh Isah Ali Ibrahim Pamtami Isah bayan wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta.

A cikin bidiyon da ke yawo, ana zargin mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara da furta kalaman da wasu ke kallon sun zubar da mutuncin Sheikh Pantami, wanda kuma dan takarar gwamnan Jihar Gombe ne a karkashin jam'iyyar PDP.

Ustaz Sanusi Asadus Sunnah Amore ya yi addu'ar Allah Ya kare martabar malamai, Ya ba su lafiya da tsayin daka, tare da rokon Allah Ya tabbatar da gaskiya, Ya kuma hada kan al'ummar Musulmi.

Lamarin dai ya jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda mutane ke bayyana ra'ayoyinsu mabambanta kan bidiyon da ake yadawa.

Abba Sani Pantami

31/07/2026

NEMAN TALLAFIN CETON RAYUWA 🚨

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai.
Ana roƙon al'umma, 'yan uwa, abokai da masu hannu da shuni da su taimaka wajen tara kuɗin jinyar Sheikh Abdul-Rashid B. Lawal Sokoto, wanda ke fama da matsananciyar rashin lafiya kuma yake buƙatar kulawar gaggawa.
Adadin kuɗin da ake buƙata domin gudanar da jinyarsa ya kai Naira Miliyan 100 (₦100,000,000). Kowane irin gudummawa, babba ko ƙarama, na iya zama sanadin ceton rayuwa.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
﴿وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ﴾
"Kuma idan na yi rashin lafiya, Shi ne Yake warkar da ni."
(Suratush Shu'ara'i: Aya ta 80).

Bayanan Asusu:
Badamasi AbdurRasheed Lawal
Banki: First Bank
Lambar Asusu: 3052574497

Allah Ya saka da alheri ga duk wanda ya bayar da gudummawa, ya yaɗa wannan saƙo, ko ya yi addu'ar samun sauƙi. Allah Ya ba Sheikh Abdul-Rashid B. Lawal Sokoto cikakkiyar lafiya da waraka. Amin.

30/07/2026

🕊️ INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah Ya yi wa Sir Abubakar Alhajin Alhaji Sardauna Sokoto rasuwa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Allah Ya karɓi ran Sir Abubakar Alhajin Alhaji Sardauna Sokoto a yau, 30/07/2026.

Muna miƙa ta'aziyya ga iyalansa, masoyansa, da al'ummar Jihar Sokoto baki ɗaya bisa wannan babban rashi. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya kuma bai wa iyalansa da al'umma haƙurin jure wannan rashi.

28/07/2026

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta tsare ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe, Jamilu Isyaku Gwamna, bisa zargin almundahanar kuɗaɗe masu yawa.

Rahotanni sun ce an gayyaci Jamilu Gwamna domin amsa tambayoyi da s**a shafi zarge-zargen da ake masa, inda daga bisani aka tsare shi domin ci gaba da bincike.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, EFCC ba ta fitar da cikakken bayani kan adadin kuɗaɗen da ake zargi ko kuma lokacin da za a gurfanar da shi a gaban kotu ba. Ana sa ran hukumar za ta ci gaba da bincike kafin ɗaukar matakin

28/07/2026

Gwamnan Kano Engr.Abba Kabir Yusuf Yaje Duniyar Mawakinsa Kosan Waka Dayake Fama Da Matsananciyar Rashin Lafiya

27/07/2026

Shin Ko Akwai Local Government Chiarman Mai Jin Tausayin Al Ummarsa Irin Hon.Yahayya Yari ?

25/07/2026

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta barranta kanta da wani mutum da ake kira Bola Mai Shaho, wanda ake zargi da ikirarin cewa yana da masaniya kan abubuwan da za su faru nan gaba.

Rahotanni sun ce mutumin ya bayyana cewa tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Hon. Munir Dan’iya, ba zai samu nasara ba, tare da yin wasu abubuwa da s**a hada da binne bakin bunsuru.

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa ba ta da wata alaka da wannan mutum ko ayyukansa, inda ta kuma bayar da umarni ga Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato da ta gaggauta kamo shi domin fuskantar matakan da s**a dace bisa doka.

Gwamnati ta kuma gargadi al’umma da su yi hattara da masu ikirarin tsafi, bokanci da sauran ayyukan da s**a saba wa addini da dokokin kasa.

25/07/2026

DAGA ZAMANI TV: Me Za Ku Ce Game da Wannan Bawan Allah, Asha? Kallo Lafiya!

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Government House Road
Abuja