Saidu usman
News and others
22/08/2022
FIRST AID GROUP OF FITYANUL OF NIGERIA
21/08/2022
MTN DATA MONTHLY 4 SALE
MTN DATA TASAYARWA
500 MB #200
1.0GB #300
2.0GB #600
3.0GB #900
5.0GB #1'500
10.0GB 3,000
CALL :08028061270
WHATSAPP 08068647430
BANK: ACCOUNT
0215678112
USMAN SAIDU
GTB
31/07/2022
Annabi Muhammad SAW yana cewa;
((لِلْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ سِتٌّ بِالْمَعْرُوفِ يُسَلِّمُ عَلَيْهِ إِذَا لَقِيَهُ وَيُجِيبُهُ إِذَا دَعَاهُ وَيُشَمِّتُهُ إِذَا عَطَسَ وَيَعُودُهُ إِذَا مَرِضَ وَيَتْبَعُ جَنَازَتَهُ إِذَا مَاتَ وَيُحِبُّ لَهُ مَا يُحِبُّ لِنَفْسِهِ)).
"Musulmi nada Haƙƙoƙi guda Shida akan ɗan uwansa Musulmi; Yayi masa sallama idan ya hadu dashi, ya amsa masa idan ya kirashi, idan yayi Atishawa yayi masa Addu'an da akeyi, ya gaisheshi idan bashida lafiya, yabi Jana'izarsa har maƙabarta idan ya mutu, yafiso masa abunda yake sowa kansa"
_Sunan Tirmizi : 2955
SHARHI
Musulunci ya kulla alaƙa ta ƴan uwantaka mai ƙarfi tsakanin yan uwa Musulmai. A matsayinmu na ƴan uwa muna zaune tare dole Akwai abubuwan da muke bukataryi domin samun daurewar ƴan uwantaka, Akwai halayyan da zamu siffantu dasu domin kara Kyautata Mu'amala a tsakaninmu. Domin haka shine Annabi Muhammad SAW yake cewa:
"Musulmi nada Haƙƙoƙi guda Shida akan ɗan uwansa Musulmi" wannan haƙƙoƙi ne Wadanda s**a zama wajibi ga kowa yana tabbatar dasu ga ɗan uwansa Musulmi.
1. "Yayi masa sallama idan ya haɗu dashi": haƙƙin musulmi ne idan ka hadu dashi kayi masa Sallama, Annabi SAW yace "Wanda yake tafiya zaiwa na zaune Sallama, wanda yake kan abin hawa zaiwa mai tafiya Sallama..." Gwargwadon fifikon halinda mutum yake yayin haduwa da ɗan uwansa toh zasu sada Amincin Allah a tsakaninsu. Girman kai da share mutane ba daidai bane. Idan kuka Sada Sallama tsakanin ku duk kun samu lada.
2. "Ya amsa masa idan ya kirashi"': idan Musulmi ya gayyaci dan uwansa wani taro na farin ciki ne dazai tayashi murna, ko na bakin ciki ne dazai tayashi jimami toh haƙƙinsane ya amsa kiran da yayi masa domin samun daurewar ƴan uwantaka da alaƙa mai kyau.
3. "Idan yayi Atishawa yayi masa gaisuwa": Addini ya koyar da cewa idan Musulmi yayi Atishawa zaice 'Alhamdulillah' wanda yajishi zaice 'Yarhamakallah' sai wanda yayi Atishawa ya kara cewa 'Yahdii kumullah...' toh idan mutum Musulmi yayi Atishawa yace 'Alhamdulillah' haƙƙinsane ka amsa masa da 'Yarhamakallah'.
4. "Ya gaisheshi idan bashida lafiya": Allah yana daura rashin lafiya ga wanda yaso a sanda yakeso, idan ɗan uwanka Musulmi yayi rashin lafiya toh wajibi ne kaje har inda yake ka gaishe dashi, bawai dole bane sai kakai masa wani abu, A'a wannan Ihsani ne da neman ƙarin Lada. Kuma basai sai ya kwanta a Asibiti ba, koda yana gidane Haƙƙinsane kaje ka gaisheshi.
5. "Ya bi jana'izarsa idan ya mutu": mutuwa tanakan kowa kuma babu wanda zai kauce mata, idan ɗan uwanka Musulmi ya mutu Hakkinsane kaje Jana'izarsa ka kuma rakashi kar izuwa Maƙwabcinsa Ma'ana Maƙabarta, kasani idan ɗan Adam ya mutu babu abinda yake bukata daya wuce ai masa Sallah a binneshi a ƙabarinsa, sai kuma anyi masa Addu'a. Toh haƙƙinsane kayi masa wannan.
6. "Yafiso masa abunda yake sowa kansa": duk abunda kakeso kafi sowa dan uwanka Musulmi wannan abun fiye da yadda kake sowa kanka. "Imanin ɗayanku baya cika har sai yafi sowa Dan uwansa abunda yake sowa kansa" kaman yadda Annabi SAW ya fada.
Dukkanin wadannan Haƙƙoƙi Ayyuka ne na samun lada kwarai da gaske babu wanda a cikinsu hadisai basuzo akansa ba, da ace zamu dawo kansu da yanzu babu wata gaba, Hassada, ƙin juna, ƙyamar juna, da fada da juna a tsakanin mu. Da duk wadannan abubuwa sun tafi a tsakanin mu. Dan Haka ina mana nuni da mukoma kan wadannan abubuwa domin kara Kyautata Mu'amalar mu da yan uwa Musulmi baki daya.
Allah ya mana muwafaƙa, ya tsayar damu kan tafarkin Addinin Musulunci, ya bamu Imani Sadiƙi, Alfarman Annabin Rahama SAW. Amin.
Yaseen Bin Hussain
07032509197
22/09/2020
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Gombe
