Lorraine Rubert
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Lorraine Rubert, Health/Beauty, Mississippi, Gusau.
17/08/2026
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana sake zaɓen gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun a matsayin wata alama cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a Nijeriya.
Shugaban wanda ya bayyana wannan a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce shi ya taya gwamnan murna a wata tattaunawar da s**a yi ta wayar salula.
Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord (A) ya ci galaba kan Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC da Najeem Salam na jam’iyyar ADC.
Ademola ya samu ƙuri’u 511,067 inda Oyebamiji ya samu 444,815 yayin da Salam ya samu ƙuri’u 17, 180.
“Sake zaɓen Gwamna Ademola Adeleke a zaɓen da aka kamalla na Osun wani tabbaci ne cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a ƙasarmu a ƙarƙashin gwamnatin jam’iyyar APC,” kamar yadda Tinubu ya bayyana a saƙon
16/08/2026
FEDERAL HIGH COURT ABUJA
Babbar kotun tarayya dake shiyar Mai Tama Abuja ta sanya ranar Talata 18/8/2026 don cigaba da sauraren karar yar takarar kujerar sanatan Zamfara ta tsakkiya karkashin jam'iyyar APC Hajiya Lubna Baba Gusau ta shigar akan rashin gudanar da zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a yankin Zamfara Central
16/08/2026
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke na jamʼiyyar Accord ya samu ƙuriʼa 511,067 don lashe zaɓen gwamnan da aka fafata ranar Asabar.
Yaya kuka ga zaɓen?
15/08/2026
Tare da wakilan yan takarar Gusau ta daya
Hon. Ibrahim Ibrahim Wambai
Hon. Abdul Bala Gusau
A cikin shirinmu na
GWANI BAIFI GWANI BA
da zaizo muku a tasharmu ta PEACE TALK TV
Dan dano daga cikin tattaunawarmu da Hon. Mustapha Jafaru kaura mataimaki na musamman ga gwamnan jihar zamfara kan kafofin watsa labarai.
Cikakkiyar tattaunarwar zatazo muku Gobe 8pm
14/08/2026
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ma’aikatan man fetur na Nijeriya cewa matatun man ƙasar, waɗanda s**a shafe shekaru da dama ba sa aiki yadda ya kamata, za su koma aiki.
Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi shugabannin Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (NUPENG) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Da yake mayar da martani kan damuwar da ƙungiyar ta bayyana, Tinubu ya ce kasancewar ana ganin wuta ko hayaƙi na fitowa daga saman matatar mai ba yana nufin tana aiki yadda ya kamata ba, yana mai jaddada cewa dole ne matatun su kasance masu samar da riba tare da samar da amfanin da aka gina su domin bayarwa.
Ya ce: “Matatun man da kuka ambata za su koma aiki.”
Tinubu ya ce ya amince ya ɗauki alhakin gyara kadarori da kuma basuss**an ƙasar da gwamnatocin baya s**a bari, ba tare da la’akari da abubuwan da s**a faru a baya ba.
Ya ce: “Ni ba mutum ba ne da zai je can, ya dawo ya ce komai yana tafiya daidai saboda na karɓi kadarori da basuss**an waɗanda s**a gabace ni.”
Ya ƙara da cewa: “Ko mene ne ya faru a shekarun baya, yanzu alhaki ne nawa a matsayina na shugaban ƙasa in gyara su, in sa su yi aiki domin amfanin mafi yawan al’ummar ƙasar. Na ɗauki wannan alhakin, kuma zan yi hakan.
14/08/2026
Nijeriya ta rasa gurbin halartar Gasar Kofin Duniya ta Mata ta 2027 a karon farko a tarihinta bayan tawagar Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu ta doke takwararta ta Super Falcons da ci 2-1 a wasan neman cancantar shiga gasar.
Nijeriya, wacce ke riƙe da Kofin WAFCON, na buƙatar ta doke Afirka ta Kudu a wasan da s**a yi ranar Alhamis a birnin Casablanca na ƙasar Maroko domin samun damar fafatawa a wasannin fid da gwani na nahiyoyi na FIFA, amma burinta bai cika ba.
Yanzu dai Afirka ta Kudu ce za ta halarci wasannin waɗanda za a buga nan gaba a wannan shekarar.
13/08/2026
Babu karamar hukumar guda da gwamnatin jihar zamfara da bata amfana da naira biliyan biyar ba (5b)
Inji Hon. Mustapha ja’afar kaura mataimaki na Musamman ga gwamnan jihar zamfara a cikin tattaunawar da mukayi dashi kuma firan zatazo muku a wannan Tasha ta PEACE TALK TV
13/08/2026
Kyaftin ɗin Argentina Lionel Messi ya bayyana cewa bai tabbatar da tsawon lokacin da zai ci gaba da taka leda ba, yayin da yake alhinin rasuwar mahaifinsa a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
A makon da ya gabata ne mahaifin Messi, Jorge, mai shekaru 68 a duniya, ya rasu bayan ya kwashe lokaci mai tsawo yana jinya.
12/08/2026
Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi na Nijeriya, Idi Mukhtar Maiha ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu jawabi a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Ya bayyana jihohin Binuwe, da Filato, da Nasarawa, da Kaduna da Adamawa, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, a matsayin wuraren da s**a fi muhimmanci saboda tarihin rikice-rikicen manoma da makiyaya da ake samu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.
Maiha ya ce gwamnati ta gano burtalai da ake kiwo guda 417 a duk faɗin ƙasar, kuma ta fara wani shiri na gwaji a Jihar Filato don gwada sabon tsarin samar da wajen killace dabbobi da nufin rage zirga-zirgar shanu.
Ya ce ma'aikatar tana tuntuɓar al'ummomin makiyaya da ƙungiyoyi kimanin 34 don tabbatar da goyon bayansu ga sauyi daga kiwon sake, zuwa kiwon dabbobin da aka tsare a waje guda.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Gusau
