Abruk
Standard at Abuja State
03/08/2026
Is Available
06/08/2025
*Yawan sakaci da addu'a yana haifar da matsala a rayuwar mutum.*
*Duk rintsi mutum ya dage dayin Azkhar safe da yamma domin samun kariya.*
*Akwai wadanda su addu'a bai dame su ba, rayuwar gaban su kawai s**a saka shiyasa ayi ta samun matsala,wani ko abu ya samesa baisan yadda zaiyi addu'a ba saboda bai saba dayin addu'a ba.*
*Mu daina wasa da addu'a kana harkan gabanka amma wani acan gefe yana jin haushin ka, yana jin haushin samun da kakeyi
16/04/2025
" Wani ko aski zai yi sai ya yi askin da Allah da manzon Allah ba su so.
Kuma sai ya ce yana son Allah da Manzon Allah. "
Abdussamad Ismail ✍🏻
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum, Hafizahullah
15/04/2025
TSARKI YA TABBATA GA ALLAH.
'Dan uwa kalli Rayuwar Duniya kalli yadda Allah ya misalta Duniyar wallahi zaka San Allah Allah ne.
Surah ta 57 aya 20
اعْلَمُوا أَنَّمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا لَعِبٌ وَلَهْوٌ وَزِينَةٌ وَتَفَاخُرٌ بَيْنَكُمْ وَتَكَاثُرٌ فِي الْأَمْوَالِ وَالْأَوْلَادِ ۖ كَمَثَلِ غَيْثٍ أَعْجَبَ الْكُفَّارَ نَبَاتُهُ ثُمَّ يَهِيجُ فَتَرَاهُ مُصْفَرًّا ثُمَّ يَكُونُ حُطَامًا ۖ وَفِي الْآخِرَةِ عَذَابٌ شَدِيدٌ وَمَغْفِرَةٌ مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَانٌ ۚ وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا مَتَاعُ الْغُرُورِ
MA'ANA:
Ku sani cewa rayuwar duniya wasa ce
(wasan Yara)
Rayuwar Duniya shagala ce
(wasan Manya, entertainment)
Rayuwar Duniya ƙawa ce
(Ado da Burgewa)
Rayuwar Duniya alafahri ce a tsakaninku (da burace burace)
Misali Nayi Abu ka za, Ina alfahari da shi ai babu Wanda ya Kai ni ko yayi Irin nawa!
Rayuwar Duniya gasar wadata ce ta dukiya da 'ya'ya, misali ni na mallaki dukiya za ka wane Kuma ya fini to nima sai na fi shi Tarawa gasar sayan Kadara ko Tara kudi, da Kuma tara 'ya'ya ana takama da alfahari da su.
Sai Allah yace Ku sani ita Duniya misalin ta Kamar shuka ne wadda yabanyarta yayi Kyau tana bayar da sha' awa ga manoma, tayi Kore san nan sai awayi gari ta ƙeƙashe, ta bushe ta zama ciyawa ta koma busas shiya ta Kone ta zamo shara abun zubarwa mara amfani.
Toh, haka Duniya take duk 'Kawan Dake cikin ta da ado da dukiya da 'ya'ya da kadara da ku ka tara, to watara sai Kun wayi gari Babu su, komai da Komai ya kare za ku koma kamar yadda ku ka zo Duniya ada Ba ku da Komai.
Allah yace Kuma a alahira akwai azaba mai tsanani ga kafirai da Masu karyata ayoyin Allah a Baki ko a aika ce.
Allah yace Kuma akwai gafara daga Allah da yardar sa ga mumimai Masu Imani da Allah da Manzon Sa da aiki da Littafin Allah.
Allah yace Kuma ita rayuwar duniya ba ta zama ba komai ba face ɗan jin daɗi ne kadan da ruɗi Mai yawa a cikin ta.
Shi yasa Manzon Allah (s.a.w) yace kuji Tsoron duniya, ku nisanci Duniya da abinda yake cikin ta, ku zauna Aduniya kamar Bako ko me tsallake Hanya.
Duniya ba tabbas karka sake ta rude ka ta shagaltar da Kai har ta mantar da Kai Lahira, ba komai ba ce face ruɗi da Kawa mara tabbas.
Saboda haka Kada ta hanaka Neman Lahira Gidan tabbas, Wallahi ka bari ta rude ka Kayi hasara.
Allah yasa mugama Lafiya Allah yasa Lahira ita ce Makurar tunanin mu ba Duniya ba.
Allah ka Gafartawa Iyayenmu mu Malumanmu, idan tamu tazo Kasa Mucika da imani Kasa aljanna ce Makomar mu da su Baki Daya.
WALLAHU A'ALAM.
Rubutawa ✍️ Yunusa Magaji Bala.
15/04/2025
ALLAH SHI KE AZURTAWA
“Ai malam tunda ka ga mahaifin mutum ya mutu, bayan mutuwar mahaifin yaron,
yaron yayi kuɗi, ƙaryane a duniya ace don ba wani baza kayi kuɗi ba”
Mallam Ahamd Tijjani Yusuf Guruntum Hafizahullah
Usman Bin Adam ✍️
15/04/2025
Manzon Allah (SAW) yace; "Babu abunda yake saurin kai mutum ALJANNAH irin abu biyu
(1) Tsoron Allah, da kuma
(2) Kyakkyawar dabia ( Hali mai kyau)
Allah yasa mu dace.
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when Abruk posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.
Subscribe
We will notify you when anything happens in Jigawa.