Sayyida Ma'asuma

Sayyida Ma'asuma

Share

JAKADIYAR IMAMU HUSSAINI (A.S)

ZAMUYI AIKI TUQURU DIMIN KARE MARTABAN IYALAN GIDAN MANZON ALLAH (S A W W)

ALLAH KADAFA MANA

Photos from Sayyida Ma'asuma's post 24/09/2026

A CIKIN KASAR AMURKA A GABAN DONALD TRUMP......!!! .. Umar Hassan Gololo...
Shugaban Jamhuriyyar Musulunci ta Iran Dakta Mas'ud Pezeskian ya daga hoton Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Shahid Sayyid Ali Khamne'i(QS), hoton jakar Makaranta alamin daliban da s**a yi shahada dalilin harin ta'addancin Gwamnatin Amurka da HKI karkashin Jagorancin Trump da Natenyahooo.
Sannan ya daga wani littafin da yake dauke da hotunan ta'addancin Gwamnatin Jikokin Birrai da Aladu akan Palasdinawa.
Ko Natenyahooo, Donald Trump da sauran azzaluman Shugabannin kasashen Duniya karnukan Amurka basu tsaya a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya sun ji ko sun kalli wannan sakon na Dakta Pezeskian ba to wallahi sai sun gani a Gidajensu har a dakunan Matansu.
Sako daga Jamhuriyyar Musulunci ta Iran zuwa ga azzaluman Shugabannin kasashen Duniya ya je garesu babu shamaki.

Photos from Sayyida Ma'asuma's post 19/09/2026

Wani yace "Kullum sai ace Iran ta kai hare hare kan Sansanin Sojojin Am¥rk@, amma ba abinda muke gani", nace su wadda ake kai musu harin ai suna gani, ba ka ga su da kan su s**a nemi tsagaita wuta ba?, yanzu kuma sun fara fito da ɓarnar da akai musu a fili, wannan wani ɓangaren sansanin Sojin Amurk@ na Kuwait bayan Syed Mojtaba ya bada umarnin ragargaje shi, Alhamdulillahi.

Photos from Sayyida Ma'asuma's post 19/09/2026

Wasu ma'aurata a Iran sun gudanar da bikin Auren su yau Juma'a wurin jaddada goyon bayan su ga nizamin Musulunci da ke iko da ƙasar.

TikTok · MUAHS Elegance Fashion& Beauty 18/09/2026

TikTok · MUAHS Elegance Fashion& Beauty TikTok | Make Your Day

Photos from Sayyida Ma'asuma's post 16/09/2026

Mayaƙan Gwagwarmayar Yemen wato Hou-thi tsaye akan jirgin yaƙin Saudi Arebiya da s**a harbo nau'in F-15SA, farashin jirgin ya kai Dala Miliyan 110. Masu yaƙi da Silifas sun kaɓo shi yau 16 ga Watan Satumba.

13/09/2026

A RIƘE MASA WANDO.

A cewar wasu kafafen yaɗa labarai na Saudiyya, Janar Tareq Saleh mai samun goyon bayan Saudi Arebiya, ya tsere zuwa Somalia bayan da Houthi s**a fatattaki sojojinsa daga Mocha (Al-Mokha).

Photos from Sayyida Ma'asuma's post 13/09/2026

ANA TA SAMUN GAGARUMAR NASARA.

Mayaƙan (Houthi) Ansarullah, na ci gaba da kwace iko da sabbin gine-ginen ababen more rayuwa na ƙasar, yanzu haka ma sun ƙwace wani ƙaramin tashar jiragen ruwa da ke kusa da garin Murad, mu taya su da Addu'a.

13/09/2026

KAYI JAN WUYA KA HUTA.

"Idan har Amurkawa mayaƙa ne, to su fuskanci rundunonin jaruman sojojinmu mu mana. Me ya sa zasu ke kai hare hare kan ababen more rayuwar fararen hula, kayan abinci da hanyoyin samun abin dogaro?. Idan kuwa su mutane ne, me ya sa suke hana mutane samun ruwa, abinci da magunguna?
Ba fa za a tilasta wa al’ummarmu mika wuya ta hanyar danniya da tsoratarwa ba. Iran ba za ta mika wuya ba."

— Shugaban Ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian.

12/09/2026

A taron, sun jaddada haɗin kai tsakanin sojojin ƙasa da IRGC, suna bayyana wannan haɗin kai a matsayin abu mai muhimmanci da zai ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen tunkarar abin da s**a kira “makircin maƙiya.”

A wannan taro, Ahmad Vahidi, kwamandan IRGC, ya ce: “Ƙarfin sojin rundunar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya zarce tunanin maƙiya. A wannan yaƙi, sun gani da idonsu cewa hasashensu na ƙarya game da ƙarfin sojojinmu ba daidai ba ne, kuma ainihin ƙarfin sojin Iran na ƙara bayyana a filin daga.”

Shi ma Babban Kwamandan Sojojin Iran, Amir Hatami, ya ce a wannan yaƙi:

“Duk wani ko da ƙaramin hari da aka kai wa Iran, sojojin ƙasa da na IRGC sun mayar da martani cikin haɗin kai, cikin sauri, cikin hikima, kuma da ƙarfi.”

Babban kwamandan sojojin ya kuma bayyana cewa Iran ba za ta yi sulhu ko sassauci kan muradunta da buƙatun ƙasa ba.

12/09/2026

HOUTHI TA FAYYACE MATSAYINTA KAN JIRAGEN RUWA A RED SEA

Mai magana da yawun dakarun Houthi, Yahya Saree, ya bayyana cewa zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin Tekun Red Sea na ci gaba da kasancewa cikin aminci, sai dai jiragen ruwa da ke da alaka da Saudiyya.

Saree ya kuma yi gargadin cewa hare-haren soji kan dakarun Saudiyya za su ci gaba da kara tsananta, har sai an kawo karshen abin da ya bayyana a matsayin katangar da aka kakabawa Yemen.

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin ci gaban dakarun Houthi a yankunan da ke kusa da mashigin Bab el-Mandeb, daya daga cikin muhimman hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa a duniya.

Har zuwa yanzu, wasu daga cikin wadannan ikirare-ikiraren na bukatar karin tabbaci daga majiyoyi masu zaman kansu.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kontagora?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Gidan Aliyu Ukuru Kasuwan Garba
Kontagora
SHI'AIMAMIYYA

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sayyida Ma'asuma posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Kontagora.