SHI'A SABON SHAFI

SHI'A SABON SHAFI

Share

Mun Bude wannan page domin isar da sakon jagora

Photos from SHI'A SABON SHAFI's post 28/06/2026

A cikin hidima ga Abi Abdullahil Husain (A,S) an shirya maukibin Shahid Qasim (R.A) yau wurin muzahar Ashura a cikin garin Sokoto. Maukibin ya raba abinci da ruwa da sauran kayan masarufi ga mahalarta Muzaharar domin neman lada ga Shahid Qasim (R.A) Muna fatan Allah y akarbe shahadar Shahid Qasim tare da sauran Shahidai gaba daya.

Photos from SHI'A SABON SHAFI's post 28/06/2026

HOTONAN YAN UWA HARISAWAN IMAM HASSAN ALMUJTABA (AS) ZONE ABOKAN AIKIN HURRASUL ZAKZAKY (H) FIRE SARVICE 🔥 🔥 🔥🔥 BAYAN KAMMALA MUZAHARAR ASHURA TA BANA

SAKKWATO UNIT DA KUMA ILLELA UNIT

21/06/2026

KASHE NI BA ZAI KAWO KARSHEN SHI’A BA, SAI DAI YA KARAWA KARBALA YAWAN SHAHIDAI

– Inji Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Na san bayan da s**a harbe mu, su kaimu nan su kaimu nan, har s**a kawo mu nan Abuja s**a kai mu asibitin jami’an tsaro. To sai s**a zozzo wajen su bakwai, kowanne ya zanzare ya zamge wuya, wai za su yi tambayoyi ne. To ba zan baku bayanin dukkan abin da ya faru ba, zan fada muku wani bangare ne na abin da nace musu.

Na ce musu, sojan da ya saka ni a mota yana ta zage-zage. Cikin abin da yace min, yau ka mutu. Sai nace masa ai kai ma za ka mutu. Sai ya yi shiru. Sai nace masa ko ba za ka mutu ba ne? Sai ya yi shiru. Sai na sake ce masa, ko ba za ka mutu bane? Sai yace, Shi’a ta kawo karshe. Ni ma sai na yi shiru. Da ya cigaba da zage-zage sai ban ce masa komai ba. Ban amsa masa cewarsa Shi’a ta kawo karshe ba, saboda na ga a lokacin shi ba yana da hankali bane, bai cancanci in ma yi magana da shi ba, tunda zage-zage yake yi.

Sai na ce ma su wadannan mutanen da s**a zo masu zanzaron nan, ku yanzu bari na fada muku, Da kashe wani mutum zai kawo karshen Shi’a, da wannan mutumin Imamu Husaini (AS) ne, wanda shi an ritsa da shi da iyalansa da sahabbansa ba su kai mutum 100 ba. Mahaya akalla dubu 30, akallan kaddarawa. Mahayi, in an ce maka rundunar mayaka, dama yana daukan akwai mahaya, akwai mayakan kafa, Faris shi ne mahayi, Rajil kuma mai yaki da kafa, to galiba idan ka ga mahaya to za ka samu Rajjal sun nunka su biyu ko uku ma. An fahimta ai. In ka samu runduna aka ce Faris dubu daya, to ka tabbata Rajjal ya kai dubu uku ko ma fiye, wato mayakan kafa.

To, abin da na fada musu, nace to akallan Taqadiri mahaya dubu 30, mafi yawan Taqadiri, da mahaya da mayakan kafa mutum dubu dari biyu, s**a far wa mutum dari daya, ba su kai ma dari daya ba, a falalen daji, s**a kashe su duk, s**a tsire kawukansu a masu. Da ainihin ana gamawa da Shi’a da karshen kenan. Amma wannan tambatsa shi ya yi, shi ne ma ya mai da Shi’ar ta kambama duk duniya.

Ina fada muku abin da na gaya wa wadannan ne, nace musu in abin ku kashe ni ne, to za ku kara wa Karbala yawan Shuhada ne, amma Shi’a karuwa ma za ta yi, don ba ni ne Shi’ar ba ballantana ku kashe ni ku ji tsit.

Su sai s**a yi shiru. Wai sun zo su yi tambayoyi ne. Nace yanzu a wannan hali, kuka tunanin za ku min tambaya? Sai na ji daya ya zunguri daya yana ce masa, ba wannan ne lokacin yi ba. To sai s**a tafi, tambayoyin da basu yi ba kenan. Sai bayan kamar shekara biyu s**a zo, s**a ji abin da s**a ji daga garemu. Wannan bazan muku bayanin dogon bayanin ba.

– Cikin Jawabin Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin ganawa da‘yan uwa kimanin 200 da gwamnatin Buhari ta tsare su lokacin Waki’ar Buhari 2015, a Abuja, ranar Lahadi 4/6/2023 (15/11/1444H)

– Sheikh Zakzaky's Library





6/Muharram/1448
21/June/2026

08/06/2026

Wanene Jagoran Harka Islamiya na yammacin Africa Kana Buda Baki zakicemin Maulaya Sayyid Zakzaky (H) .

Hakika kafadi Gaskiya Kuma kana kan dai dai Amma Babban abin duba anan shine Suwaye Mataimakansa karka cemin Hurras, Abul fadal Abbas, Jasaz, Intizar Imamul mahdi (ATF) 🫡,Kashshafatul Imamul hujja 🫡, Da sauransu .

Suna cikin Mataimakansa Amma Suwaye Hakikanin Mataimaka

Wannan Tambayar ba kowa keda Amsartaba "abinda yasa nace maka haka kuwa Idan aiki ne da Himma da dagiya bazaka Kai Abul fadal Abbas ba idan Kuma juriya ce bazaka kai Sayyada Zainabul zubra ba idan Kuma Sadaukar wace wakai Nan ka kaiga Koda nunfashin Imam Hussaini a filin karbala "

Allah karka sauyamu da wasunmu a cikin wannan tafiyar Allah kayi Amfani damu wajan Taimakon Jagora Allah kasa muzamu tamkar su Shahid Ahmad Zakzaky wajan Kare Maulaya Zakzaky (H)

Photos from SHI'A SABON SHAFI's post 22/05/2026

KAITSAYE DAGA HUSSAINIYA IMAM MAHDI (ATF) DAKE UNGUWAR MABERA SAKKWATO

An gudanarda Karatun Ta'alim kamar yadda aka saba a Duk Alhamis Wanda Wakilin Yan uwa Almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) Na Yakin Sakkwato yagabatar .

( Inda Shaikh Sidi Munir ya gabatar da karatu Akan Muhimmancin Kwanakin Nan Goma na Farkon Watan Zulhijja da kuma Ayyukan Ranar Hawan Arfa Wanda ya hada Addu'a sallolin Nafila Masu Tarin Daraja .

Shaikh ya yayi kira ga Wanda yakeda Littafin Mufatihul janaf da yayi kokari yayi Photo copy Ya rabawa wadanda Basu samu damar mallakar nasu Littafin Mufatihul janaf ba .

Shaikh Sidi Munir Sakkwato yakara da nuni akan cikin kwanakin Nan Akwai Na tsarkin ba kamar na yau da kullum ba Azumi haka Kuma akwai karanta ziyara kamar Ziyarar Amirul muminina Imam Ali (as), Ziyarar Ashura ta imam Hussaini (as), Sai Kuma Addu'ar Ummu Dawud .

Kwamitin Zaman Makokin Ashura sun tunatar Akan Alkawullan da Yan uwa s**a dauka na Bada Tallafi Akan Zaman juyayin Kisan Jikan Ma'aikin Allah Imam Hussaini (as) na Shekara Mai zuwa Domin Ganin Zaman Ya gudana Yadda yakamata.

Allah yabada Ikon Sauke Nauyi Bihakki Sahibul asr 🫡🇵🇸🇳🇬🇮🇷

Ga Wasu daga cikin hotonan da muka dauka muku

Photos from SHI'A SABON SHAFI's post 19/05/2026

KAITSAYE DAGA HUSSAINIYA IMAM MAHDI (ATF) DAKE UNGUWAR MABERA SAKKWATO

An gudanarda program na Auran Sayyada Zahra (sa) da Mijinta Imam Ali bin Abutalib a Dairar Sakkwato Wanda Sister forum s**a Shirya Kuma s**a gabatar

Malam Sidi Munir Sakkwato Shine yayi tsokaci akan Auran Sayyada Zahra da Mijinta Imam Ali

Shararran Mawakin Alhul baitin nabiyu Alh Umar Na ma'aiki shine ya gabatarda majalisin a wajan .

Photos from SHI'A SABON SHAFI's post 19/05/2026

Auren Sayyida Fatima Zahra Da Imam Ali (as); An Shirya Ƙasaitaccen Biki a Da'irar Kudan.....

Dandalin Sha'iran Kudan Tare Da Haɗin Guiwar Rundunar Sayyida Zahra Da ke Da'irar Kudan Sun Shirya Tare Da Gabatar Da Ƙasaitaccen Biki Domin Murna Da Wannan Aure Mai Tarin Albarka Wanda Allah (swt) Ya Ɗaura Shi a Irin Wannan Rana Ta 1 Ga Watan Zulhijja.

Taron An Fara Shi Ne Jiya Lahadi 17 Ga Watan Mayun shekarar 2026, Da Gasar Waken Bege Akan Imam Ali Da Sayyida Fatima Zahra (sa). Matasan Mawaƙa Daga Ciki Da Wajen Garin Na Kudan Sun Yi Musharaka a Wannan Gasa Kuma Sun Nuna Bajintar Su Tare Da Bayyana Baiwar Da Allah Ya Masu Na Waken Bayin Allah.

A Yau Litinin 18 Ga Watan Mayun shekarar 2026 Wanda Tayi Daidai Da 1 Ga Watan Zulhijja Aka Yi Khatmar Wannan Taro. A Yayin Wannan Taron An Bayyana Zakarun Wannan Gasar Tare Da Karrama Su Da Shaida Ta Musamman Domin Ƙara Masu Kwarin Guiwa Akan Wannan Al'amarin.

Mallam Aminu Ibrahim Ya Gabatar Da Takaitaccen Jawabi Akan Yadda Auren Na Sayyida Zahra Da Imam Ali Ya Kasance Tare Bayyana Shi a Matsayin Aure Mafi Daraja. Daga Karshe An Yanka Alkaki Tare Da Abincin Walima Sannan Aka Yi Addu'a Aka Sallami Kowa.

©️Zaria Media Forum
18th May 2026
1st Zulhijja 1447

19/05/2026

```Auren Sayyida Zahra da Imam Ali ba kawai haɗuwar masoya biyu ba ce, haɗuwa ce ta tsarkin zuciya, imani da soyayyar da ta ginu akan biyayya ga Allah!.. 🌼🥀

Soyayya mafi kyau ita ce wadda take kai mutum zuwa ga alkhairi. A irin wannan rana mai albarka, muna tuna auren Ali da Zahra, gidan da aka gina da soyayya, hakuri, ibada da mutunci. Allah Ya albarkaci dukkan soyayya mai tsafta da niyya ta gari. 🤍✨```

18/05/2026

Ya sahibaz zaman

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Victoria Island?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Kalambaina
Victoria Island
BBB