Real Mustapha Musa

Real Mustapha Musa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Real Mustapha Musa, Health/Beauty, Dogon Dawa, Abuja.

28/08/2022

"...Duk lokacin da kaji ƙarya cikin zuciyar ka sai kaji cewa gaskiya ce, sai dai wani don zuciyar ka ya sa ka ƙi (ka karkata) zuwa ga ƙarya.."

-Malama Zeenatuddeen Ibrahim (Ummus-shuhada) yanzu a Mu'utamar a Birnin Niamey.

28/08/2022

AYI TA DAMUN SISTER SE TA SANYA HIJABI

A matsayin ka na uba! Sau nawa ka taɓa sayawa 'Yarka Hijabi.? Haƙƙin sayan Hijabin ya rataya a wuyan waye.? Ya rataya a wuyan mahaifi ne, kai uba! Haƙƙi ne a kanka ka sayawa iyalan ka Hijaban da zasu Sanya su lulluɓe jikkunan su, Kamar yadda Allah ta'ala ya umurta. Za'ayi ta magana akan Sister tayi ƙoƙarin sanya ingantaccen Hijabi abin takaici baza a taɓa chalengen ɗin iyaye maza ba, shin suna ƙoƙarin sayawa iyalan na su Hijabai, da safan da zasu riƙa Amfani dashi yauda Kullum. Da yawan Iyaye maza basa sayan Hijabin sedai uwa! ko 'Yar ta sayawa kanta.

Mata ko 'Ya, basu ne Allah ta'ala ya rataya musu, su sayawa Kansu kayan da zasu tsare tsaraicin su ba. Mahaifi shi yake da haƙƙin da zai sayawa 'Yarsa Hijabai da sauran abubuwan da 'Ya mace take buƙata in takai shekarun Takalifi. Daga Ranar da ace 'Ya, mace ta huce Shekaru tara 9 a duniya to hukuncin Allah ya sauka a kanta, in zata fita dole ta sanya safa da Cikakken Hijabi (lulluɓi) kai a matsayin ka na mahaifi kana kula da hakam?, kana sayawa 'Yar ka, abubuwan da ɗiya mace take buƙata in takai wannan minzalin.?

Matarka kai ka Auro! 'Ya mace kai ka haifo! Wajibi ne ka Kula dasu. Ka ciyar dasu, ka shayar dasu, ka tufatar dasu, ka iliman tar dasu. Ɗawainiyar 'Yarka mace baze taɓa tashi daga wurin ka kai (mahaifi) ba, har se Ranar da ka auran da ita, kamar yadda ka Auro mahaifiyar ta. 'Yarka takai shekaru 12 kuma kasan duk 'Ya mace in takai wannan minzalin akwai abubuwan da take buƙata. Wajibcin iyaye maza ne su riƙa sayawa 'Ya 'Yansu mata Hijabai da kayayyakin da suke buƙata in su zama mukallafai, Allah ta'ala ya dafawa iyayen mu baki ɗaya ya Basu iƙon sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.

~Daga me kishin Sista me burin Auren Sista © — Reall Mustapha Musa

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Culinary Team

Attire

Website

Address


Dogon Dawa
Abuja