Tanko Alhaji Maigida
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tanko Alhaji Maigida, Health/Beauty, Tafawa Balewa LG, Bauchi.
28/07/2026
TORO TA ZAƁI JAGORA, BA KUDI BA
Al'ummar Ƙaramar Hukumar Toro sun sake nuna cikakkiyar ƙauna, amana da goyon baya ga Makama Babba, Mohammed Abdullahi Abubakar SAN, ta hanyar fito wa da zuciya ɗaya domin maraba da shi, Wannan ya tabbatar da cewa siyasa ta gaskiya ba ta ta'allaka a iya raba kuɗi ba, sai dai kan zaɓen shugaba nagari mai hangen nesa, gaskiya da ƙwarewar da kawo ci gaba mai ɗorewa ga al'umma
Toro ta nuna cewa jama'a sun fi son shugaba mai nagarta wanda zai inganta rayuwar su ta fuskar ilimi, lafiya, noma, hanyoyi, tsaro da tattalin arziki, maimakon wanda zai nemi sayen amincewar su da kuɗi na ɗan lokaci
Muna miƙa godiya ta musamman ga Hon. Bala Abdu Rishi, memba a Toro Lame Conspiracy, bisa irin gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban al'umma, musamman gina makaranta da kuma ofishin 'yan sanda, wadanda mai gidan Makama Babba ya Bude su a Jiya, Haka kuma muna yaba wa Hon. Farouk Sale Toro, ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar Toro, bisa jajircewa da yayi wurin ganin al'ummar sa sun fito kwansu da kwarkwatan su domin maraftan Makama Babba
Godiya ta musamman ga dukkan masu ruwa da tsaki, da shugabannin Jam'iyar APC da matasa, da mata da ɗaukacin al'ummar Ƙaramar Hukumar Toro bisa irin tarba mai cike da ƙauna da s**a yi wa Makama Babba, Wannan goyon baya alama ce ta nasara, kuma da yardar Allah zai zama tubalin nasaran da zata kawo wannan shugabancin da zai sake gina sabuwar Bauchi insha Allahu
I Stand With Makama Babba🥰🥰🥰✌️
02/02/2026
Jiya Lahadi 1/2/2026 Alh Murtala Ibrahim Danmalikin Boto, Ya Jagoranci Taron Wasu Rukuni Daga Cikin Magoya Bayan Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi M.A Abubakar SAN.
Rukunonin Da S**a Tarun Sun Hada Da Tsofaffin Kwamishinonin Da S**ayi Aiki Karkashin Gwamnatin Mai Girma M.A Abubakar SAN. Sai Tsofaffin Shugabannin Kananan Hukumomi Da S**a Jagoranci Kananan Hukumomin Su Lokacin Gwamnatim M.A Abubakar SAN. Sai Tsofaffin Masu Bada Shawari/ Da Masu Tallafa Na Musamman, A Lokacin Gwamnatin M.A Abubakar SAN. Sai Tsofaffin EXCO Da Sabbi A Bangaren Jam,iya.
Yayin Taron Danmalikin Boto Ya Tabbatar Wa Mahalarta Taron Cewa Mai Girma Tsohon Gwamna M.A Abubakar SAN Ya Gama Dukkannin Shirye Shirye Kuma Dayyi Takara Da Izinin ALLAH Kuma Dayyi Nasara.
Bayan Jawabin Shugaban Taron, Ansamu Wakilci Daga Dukkan Rukunoni Das**a Taru Wanda S**ayi Jawabin Jindadin Wannan Sako Na Takaran M.A Tare Da Nuna Goyon Bayansu Dari Bisa Dari (100%} Amadadin Rukunin Dasuke Wakilta.
Taron Ya Sanya Farin Ciki Da Jindadi Wa Magoya Bayan Na M.A Inda Kowa Ke Cewa Daman Wannan Sakon Suke Jira Don Daukan Mikati Tare Da Isar Da Wannan Babban Sakon Wa Alumman Su.
Daga Karshe An Rufe Taro Da Addu,an ALLAH Ya Dawo Mana Da Gwamnatin Mai Girma Tsohon Gwamna Muhammed Abdullahi Abubakar SAN. AMEEN
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Tafawa Balewa LG
Bauchi
