Gidan kamshi General Enterprise
Turaren wuta, humra, badra,& etc
HUMRA TA ASALI NA ƳAN MAIDUGURI ✨
Kamshi ne mai ɗaukar hankali da zarar an shafa. Kafin ma ki fito waje, ƙamshin sa zai riga ya sanar da isowarki. Humra ce mai daɗin ƙamshi, mai k**a jiki kuma mai ɗorewa.
Idan kina son kamshi na musamman wanda zai sa mutane su juya suna tambayar me kika shafa, to wannan Humra ta ƴan Maiduguri ya dace da ke.
Kamshi mai daɗi
Mai ɗorewa Mai k**a jiki
Na asali daga Maiduguri
Duk mai buƙata tayu min magana domin yin oda.
Kina ganin turaren wuta mai madarar turare sosai a ƙasan kwalba kina tunanin shi ne mafi ƙam shi? To bari ki ji gaskiya...
24/06/2026
Mutane da yawa suna ganin idan madarar turaren wuta yayi yawa har ya kwanta a kasan kwalba, to wannan ne alamar cewa turaren ya fi ƙamshi ko ya fi inganci. Amma gaskiyar magana ba haka abin yake ba.
A zahiri, idan aka yi amfani da madarar turare fiye da kima ko wadda bai dace ba, hakan kan sa turaren ya yi kauri sosai. Wasu lokutan ma idan aka ɗora shi a kan gawayi, ba ya bada ƙamshin da ake tsammani saboda nauyin madarar turaren da aka yi amfani da shi.
Abin da ya fi muhimmanci ba yawan madarar turaren ba ne, sai ingancin turaren da kuma irin madarar da aka yi amfani da ita. Ba kowani madarar turare bane ya dace da turaren wuta, kuma ƙwararriyar mai haɗa turare tasan adadin da ya dace domin a samu ƙamshi mai daɗi, ɗorewa da kuma inganci.
Saboda haka, kada ki auna ingancin turaren wuta da abin da kika gani a kasan kwalba kawai. Auna shi da ƙamshin sa, ɗorewar sa da kuma yadda yake bada ƙamshi idan aka saka shi a kan gawayi.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Gwange Layin Mamman Shifta Street
Maiduguri
1
