Sheikh Sidi Munir Sakkwato

Sheikh Sidi Munir Sakkwato

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sheikh Sidi Munir Sakkwato, Health/Beauty, Sokoto.

Photos from Sheikh Sidi Munir Sakkwato's post 29/05/2026

Sheikh Sidi Munir Sakkwato wakilin yan'uwa musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Yaqoub Alzakzaky (H) Malam Muhammad Illela sun kai ziyarar jaje ga al'ummar musulmi da harin Sojoji ya rutsa dasu a kauyuka shida na Illela wanda ya hada Runji da sauransu.

Al'ummar kauyukan da s**a hada maza da mata da kananan yara sun yi gudun hijira zuwa garin Kalmalo dake cikin karamar Hukumar Illela ta jahar Sakkwato.

Ga Hotunan Ziyarar a Kasa.

28/05/2026

Daga Masallacin Idin Babbar Sallah.

Photos from Sheikh Sidi Munir Sakkwato's post 27/05/2026

Daga Masallacin Idi anan cikin garin Sakkwato.

Allah Ta'ala ya maimaita mana ta badinbadada.

09/05/2026

Ziyarar Hubbaren Mujaddadi Shehu Usmanu Bn Fodiye dake Sakkwato.

09/05/2026

Majalisin Barhama Gombe a Sakkwato.

Photos from Sheikh Sidi Munir Sakkwato's post 09/05/2026

Zawiyar Aliyu Tailah ta kungiyar Shababu FHaidah Al’inyasiyya reshen jihar Sakkwato, sun shirya gagarumin Majalisi wanda s**a gayyato shahararren mawakinnan Barhama Gombe.

Majalisin da ya gudana a jiya Juma'a 8/5/2026 a Unguwar Tudun Wada (Majema) dake cikin garinSakkwato.

Wakilin yan'uwa musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem Yaqoub Alzakzaky (H) na yankin Sakkwato Sheikh Sidi Munir ya sami halartar Majalisin.

Allah Ta'ala ya kara hada kan al'ummar musulmi.

24/11/2023

Manufar Kiranmu. Tare da Sidi Munir Sakkwato.

Daga, Bilal Nasir Umar Sakkwato.

“Akwai dayawa waɗanda basu san haƙiƙanin abinda muke kira akai ba, ko saboda sun mana nisa ko kuma an kange su da su zo su raɓemu, sai kuma ya kasance a kodayaushe wani abu ake gaya musu daban akanmu saɓanin abinda muke kira ɗin, wanda wannan dalilin ne yasa muka zaɓi samar da wani lokaci domin yin bayanin haƙiƙanin abinda muke kira akai domin al'umma ta ji daga garemu.”

“Wannan kira ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibrahim Yaqoub Alzakzaky (H) kira ne na komawa Allah (T) domin sanin kanmu ne wannan yanayi da muke ciki mun yi nisa da biyar dokokin Allah (T), yanzu al'ummar nan tana yiwa dokokin Allah shan koko mai zafi a maimakon mu yi abinnan da Allah (T) yake cewa “Ya ayyuhallazina amanu udhulu fissilmi kaffa” ya ku waɗanda kuka yi imani ku shiga musulunci ga baki ɗaya sai muka kasance muna aikata wasu dokokin na Allah muna barin wasu kamar yadda anan ma Allah (T) yake cewa, “Afatu'uminuna bi ba'adil kitabi watakfuruna biba'ad” shin zaku yi imani da sashen littafi ku kafircewa sashe, ma'ana ku yi Sallah ku yi Azumi baku katse hannun ɓarawo baku bulale mazinaci ko jefewa da sauran ire-iren waɗannan dokokin da sunanan karantawa kawai ake yi a cikin alƙur'ani amma ba'a aikatawa.”

“Addinin nan kamar yadda muka sani yazo mana ne ta hannun Annabin tsira (S) sannan kuma ba haka kawai addinin yazo mana ba domin mu aikata abinda muke so a lokacin da muke so ko muka ga dama ba, a'a akwai ƙa'ida, Allah (T) ya gaya mana a cikin Alƙur'ani mai tsarki cikin suratul Ahzab cewa, “Laƙada kana lakum fi rasulillahi usuwatun hasana Liman kana yarjullaha walyaumil ahir” haƙiƙa Manzon Allah ya kasance kyakkyawan abin koyi gareku amma ga mai ƙaunar ya sami gamuwa da Allah maɗaukakin sarki ya sami sakamako a ranar Lahira, haka kuma kamar yadda Allah (T) yake sake gaya mana cewa, “Wama atakumur rasul fahuzuhu wama nahakum anhu fantahu” wato abinda Manzo ya zo muku dashi ku riƙa wanda kuma ya haneku ku hanu.”

“Anan zamu ƙara fahimtar cewa addinin nan ba abinda muka tsinta kawai bane yazo da ƙa'idodi, sannan yazo da abinda ake buƙatar mu ɗabbaka wanda idan muka kalli rayuwarmu ta yanzu muka kalli abinda Annabin shiriya (S) yazo dashi, sai mu ce a halin yanzu al'ummar musulmi mun rabu da cikakken addinin da Allah maɗaukakin sarki ya aiko Annabi (S) da cewa mu aikata a bayan ƙasa domin mu je gobe ƙiyama mu sami kyakkyawan sakamako.”

“Allah ya rayar da zukatanmu ne ta hanyar ji daga wannan bawan Allah da ya tayar a wannan nahiya Sheikh Ibrahim Yaqoub Alzakzaky (H) yake kuma kira fiye da shekaru arba'in wanda kuma a wannan ƙasar ba wanda bai sami labarinsa ba sai dai ta yuwu wani ya sami labarinsa akasin abinda yake kira.”

“Allah (T) ya kan aiko Manzanni lokaci bayan lokaci idan al'umma ta canza ta hanyar sake tayar da wani Manzo domin sake jaddada saƙon na Allah (T), yanzu kuma da aka cika Manzanci babu wani Manzo baya ga Annabi (S) to a duk lokacin da al'umma ta kuskure ta canza, Allah (T) ya kan tayar da Mujaddadi domin ya sake jaddada addini kamar yadda Allah ya tayar da Mujaddadi Shehu Usmanu Bn Fodiye a wannan nahiya saboda raunin da musulunci ya yi, domin a lokacin ga littafin Allah ga kuma musulmi amma basa bin tsarin Allah, sai Shehu ya tashi ya yi kira har Allah ya tabbatar addini a wancen lokaci duk da muzgunawa da cutarwa da Shehu ya fuskanta ga sarakunan lokacinsa wanda kuma a halin yanzu shima Allama Sayyid Zakzaky (H) yana kira ne zuwa ga bin littafin Allah kuma cikin ikon Allah shima shuwagabannin wannan lokaci suna amfani da irin wancen salo da sarakunan lokacin Shehu s**a ɗauka kansa na ƙoƙarin murƙushe kiran nasa kwabo da kwabo.”

“Ga matsalolin rayuwa nan sun yiwa al'umma katutu, na yau daban na gobe daban, dama Allah (T) yana cewa, “idan musulmi s**a daina bin littafinsa mai tsarki to zasu sami rayuwa mai ƙunci, rayuwarsu zata kasance ƙara bara da bana”, kuma idan muka lura dakyau yanayin da muke ciki kenan, domin idan ka duba inda aka fito kullum ƙara mulkin wane da wane ake cewa har ya zuwa Yau, nan kusa ma zamu ga abinda muke siya naira Goma a bara yanzu ya koma Ashirin. Mafitar wannan ƙuncin kuwa shine komawa tsarin Allah da Manzonsa (S).”

“Kuma wannan kira da wannan bawan Allah ke yi tsawon shekaru kira ne na kowa da kowa ba tare da la'akari da ɗariƙar da ka fito ba domin duk da bambance-bambancen da yake tsakaninmu to akwai tushen da ya haɗa mu shine Alƙur'ani da saƙon Manzon Allah (S) kuma duk lokacin da aka ce an wayi gari ba a binsa to komi tinƙahon da kake yi da mazhabarka to ganye ne ka riƙe ka saki tushe. Wasallam.” Juma'a 10/9/2022.

09/08/2023

Ku Ji Abinda Muke Kira Daga Garemu Ba A Bakunan Maƙiyanmu Ba.

Tunatarwa kamar yadda aka saba a kowace ranar Talata tare da Sheikh Sidi Munir Sakkwato, dangane da manufar kiran Sheikh Zakzaky (H).

–Talata 08/08/2023.

19/07/2023

Ku Ji Abinda Muke Kira Daga Garemu Ba A Bakunan Maƙiyanmu Ba.

Tunatarwa kamar yadda aka saba a kowace ranar Talata tare da Sheikh Sidi Munir Sakkwato, dangane da manufar kiran Sheikh Zakzaky (H).

–Talata 18/07/2023.

15/10/2022

Sanarwar Taron Makon Haɗinkan Al'ummar Musulmi A Sakkwato.

Ana sanar da dukkanin ƴan'uwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Alzakzaky cewa, gobe Lahadi 20 ga watan Rabi'ul Auwal shekara ta 1444, daidai da 16 ga watan Oktoba shekara ta 2022, za a soma taron makon haɗinkan al'ummar musulmi a Sakkwato.

Taron da zai soma gudana da misalin ƙarfe 4 na yamma a muhallin Hussainiyyatul Imamil Mahdi Atf dake Unguwar Mabera.

Babban baƙo kuma mai jawabi a wannan ranar shine, Malam Ƙasim waƙilin ƴan'uwa musulmi almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Alzakzaky na garin Tsafe ta jahar Zamfara.

Fatar ƴan'uwa zasu bada haɗinkai gurin halarta kan lokaci.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Sokoto?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Sokoto