Jaridar Basakkwaciya

Jaridar Basakkwaciya

Share

Domin ilmantarwa faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa.

30/09/2023

Assalamu Alaikum

08/08/2023

🛑 Niger.

Ƙungiyar dattawan Arewa na neman Ecowas ta cire wa Nijar takunkumai. BBC Hausa

08/08/2023

Ban Yi Nadamar Ziyarar Imam Husaini As A Iraqi Ba.–Cewar Mawaƙi Mal. Isah Babi Sakkwato.

Daga, Bala Ahmed Sakkwato.

A wata sabuwar waƙa da ya fitar mawaƙin Ahlulbaiti (As) Isah Babi ya bayyanawa masoyansa cewa, yana nan a Ɗariƙar Ƙadiriyya kamar yadda aka sani ba kamar yadda wasu ke faɗa cewa ya koma Shi'a ba.

A kwanakin baya ne dai wasu s**a riƙa yayata cewa mawaƙin ya je Iran karɓo kwangilar Shi'a bayan da wani faifan bidiyonsa ya bayyana a ƙasar Iraqi inda yake rera waƙen yabon Nana Fatima (S.A).

Duk acikin waƙar mawaƙin ya bayyana dalilin zuwansa Iraqi ba Iran ba kamar yadda masu yaɗa sharri akansa suke faɗa, inda yake cewa, “na je Saudiyya ba adadi na ziyarci Ma'aiki (S) da Sayyidina Abubakar da Umar (R.A) da Imam Hassan (As) ya fi a ƙirga, shine na yi tambaya, ina ƙabarin Imam Husaini (As), aka gayamin yana Iraqi sai na je don in ziyarcesa, amma abin haushi wasu sun riƙa yayatawa wai na je Iran karɓo kwangilar Shi'a.” injishi.

Mawaƙin bai tsaya anan ba ya jefa tambaya ga masu ƙaƙaba masa kalmar Shi'a da cewa, “Shin ko an barwa Shi'a Ahlulbaiti (As) ne domin na ji a cikin masu s**a ta suna cewa, ‘ina faifayewa gurin yabon Nana Fatima’ ?.”

Haka kuma a ƙarshe ya baiwa dukkanin masoyansa haƙuri dangane da yadda aka riƙa cin zarafin su tare da tabbatar musu cewa har yanzu yana nan a Ɗariƙarsa, tare da ƙara shaida musu cewa ziyarar Imam Husaini (As) ya je yi Karbala, kuma a yayin ziyarar ma har ya sami ziyartar wasu ƙaburburan bayin Allah irin su Annabi Adamu da Annabi Nuhu (AS), ya ƙara da cewa, “babu maƙiyin yabon Ahlulbaiti sai shashasha, mu masoya Ahlulbaiti (As) ne kuma ba zamu taɓa yin yabo bamu sanya su ba, haka kuma ziyarar da na je ko kaɗan bana nadama.”

02/11/2022

Ana zargin tsohon Kwamishina a jihar Bauchi da kisan mahaifn yarinyar da yake so
____________

𝐃𝐚𝐠𝐚
𝐍𝐚𝐬𝐢𝐫𝐮 𝐇𝐚𝐬𝐬𝐚𝐧 𝐘𝐚𝐥𝐰𝐚, 𝐁𝐚𝐮𝐜𝐡𝐢

Hukumomin tsaro a jihar Bauchi na ci gaba da tsare tsohon Kwamishina a ma'aikatar watsa Labarai ta jihar Bauchi wato Alhaji Injiniya Damina Muhammad (Galadiman Dass) a bisa zargin kisan wani bawan Allah mai suna Adamu Babanta, tsohon direba wanda ya yi ritaya a shekarar da ta gabata mai shekarun haihuwa 67 ta hanyar fisgar sa da mota yayin da yake kokarin tserewa bayan an gano yana kokarin lalata diyar mamacin.

Wakilinmu ya labarto mana cewa lamarin ya faro ne bayan da diyar mamacin mai suna Khadija Adamu Babanta 'yar shekaru 18 da ke zaune a unguwar Yalwan Makaranta a cikin garin Bauchi ta kai korafi wa mahaifin akan cewa Injiniya Damina ya matsa yana neman lalata da ita a ranar Lahadin da ta gabata, kuma ya buga mata waya akan ta same shi a unguwar Yalwan Tudu daura da gidan mai na ATIL kusa da Jami'ar ATBU. Domin tabbatar da maganar yarinyar, sai Adamu Babanta ya bukaci yarinyar ta je ta same Injiniya Damina, inda shi kuma mahaifin ya bi ta a baya.

Cikin bayanin da Khadija Adamu Babanta ta yi wa jaridar Amana yayin da take cikin tsananin alhini da kuka, ta ce bayan da ta isa wurin da yamma gab da sallar Maghariba sai Injiniya Damina Muhammad ya bude mata kofar motarsa kana ya bukaci da ta shiga. To amma ba ta shiga ba, inda ta ce masa tana jiran mai mashin ya kawo nata sako ne, kuma ana haka ne sai mahaifin nata ya iso. A cewar ta, isowarsa ke da wuya sai ya ce masa "Galadima ni ne za ka ci amanata?" Ganin Adamu Babanta ba zato ba tsammani da kuma abubuwan da yake fada ya sa Injiniya Damina ya yi kokarin tada mota domin tserewa, yayin da shi kuma marigayi Adamu Babanta ya rike motar ta baya, sakamakon fisgar motar da Injiniya Damina ya yi, motar ta fisgi Adamu Babanta tare da hada shi da gefen kwalbati, abinda ya sa ji munanan raunuka.

Duk da an garzaya da shi asibitin koyarwa na jami'ar ATBU, malam Adamu Babanta ya riga mu gidan gaskiya. To sai dai ba yi jana'iza wa mamacin ba sai a safiyar ranar Talata sakamakon bincike da likitoci s**a yi wanda rahotonsu ya tabbatar da cewa marigayin ya mutu ne sakamakon karyewan da kashin hakarkarin sa ya yi da kuma karaya biyu a kafarsa da karin wasu raunuka.

Wakilinmu ya ce an jibge jami'an tsaro a unguwar ta Yalwan Makaranta bayan da matsa s**a fara zanga-zanga akan kisan marigayin.

Kakakin rundunar yansanda na jihar Bauchi, DSP Ahmad Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce suna tsare da wanda ake tuhuma domin gudanar da bincike.

Marigayi Adamu Babanta ya rasu ya bar mata uku da 'yaya a kalla 20.
Tags

Photos from Jaridar Basakkwaciya's post 18/09/2022

Matsalar tsaro: Gwamnatin Katsina ta horas da ƴan banga 1,000

Miye ra'ayin ku akai ?

09/09/2022

TIRƘASHI: An Fasa Aure Ana Saura Sati Ɗaya Ɗaurin Auren Wata A Jihar Sokoto Bayan Iyayen Yarinyar Sun Gano Angon Ya Taɓa Samun 'Spill Over' A Jami'a

Iyayen yarinyar sun ce sun ɗauki wannan mataki ne domin suna tsoron kar a haifar musu jikoki d@ƙiƙai.

Me za kuce?

07/09/2022

Jami'an yan sanda a jihar Osun sun gudanar da zanga-zanga saboda rashin biyansu albashi tsawon watanni 18 yanzu.

Yan sandan sun koka cewa a yanzu yan achaba da masu adaidaita suna kwanciya da matansu saboda su sun gaza daukar dawainiyansu da na yara.

Jakadan Amurka na musamman ya isa Habasha don sasanta rikicin Tigray 07/09/2022

Jakadan Amurka na musamman ya isa Habasha don shiga tsakani da nufin kawo karshen sabon yakin da ya sake barkewa tsakanin 'yan tawayen Tigray da dakarun gwamnatin kasar.

Miye fatanku akan wannan ziyarar?

Jakadan Amurka na musamman ya isa Habasha don sasanta rikicin Tigray Jakadan Amurka na musamman Mike Hammer ya isa Habasha don tattaunawa da gwamnatin kasar a wani yunkuri na ganin an sulhunta bangarorin da ke yakar juna da nufin tsagaita wuta a sabon yakin da ya sake…

Photos from Jaridar Basakkwaciya's post 06/09/2022

Na San Babu Dan Pi Din Da Idan Ta Fashe Ba Zai So Ya Auri Irin Wannan Yarinya Ba

Miye ra'ayin ku akai ne ?

Photos from Jaridar Basakkwaciya's post 06/09/2022

Garin dadi : Uwargidan Shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ta Gina katafaren asbitin karbar magani kyauta a garin Yengoa na Jihar Bayelsa,

Sannunku Yan arewa😁

Daga : Abdul Journalist

Boris Johnson ya yi bankwana da fadar Downing Street bayan murabus 06/09/2022

Firaminista Boris Johnson ya mika takardar murabus ga sarauniyar Ingila bayan matsin lamba daga ministocinsa lamarin da zai bai wa Liz Truss damar zama sabon Firaminista.

Boris Johnson ya yi bankwana da fadar Downing Street bayan murabus Firaminista Boris Johnson ya mika takaddamar murabus dinsa ga Sarauniya Elizabeth ta biyu yau talata, lamarin da ke bayar da dama ga Liz Truss don sabon Firaminisan kasar.

05/09/2022

'Yan Sanda Sun Cafke Saurayin Da Ya Yi Sata A Gidan Surikansa Dake Jihar Katsina

Rundunar 'yan sanda ta jihar Katsina ta cafke Abdullahi Umar dan shekara talatin da daya, dan asalin garin Kari a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna bisa zargin satar kayayyakin sanya wa a gidan su yarinyar shi da ya zo bakunta.

Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya yi baje-kolinsa a helkwatar rundunar da ke cikin garin Katsina.

A lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Abdullahi Umar ya ce mun hadu da ita a kafar sada zumunci ta Facebook, na ce mata zan zo Katsina ta ce in zo, na shirya na zo, ta tarbe ni hannun bibiyu, na kwana biyu a dakin yayanta, cikon na ukku da zan tafi na sace na'urar mai kwakwalwa ta laptop da hulunan sa ukku da kayan sawa. Na shiga gudan dakin na dauki takalman sawa kafa ukku, a cewarsa. Ya Ubangiji yatsaremu da aikin da nasani amin

Daga Isma'il Muhammad Goje

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Sokoto?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Sokoto
1615023