Elaaj Sirrin Lafiya
Sirrin Lafiya🧑⚕️ da Magungunan Halitta 🌿 | Shawarwari kan Lafiyar Jiki, Kwakwalwa da Rayuwa Mai Kyau a harshen Hausa.
18/04/2026
Kun yarda da hakan kuwa? 🤔🤔🤔
WANE IRIN MADUBI NE KUKE NUNA WA YARON KU?
Muna yawan korafi cewa yaranmu ba sa jin magana, suna da taurin kai, ko kuma suna kwaikwayon halayen banza.
Amma kun taba tambayar kanku: "A ina s**a dauko wannan halin?"
Ko kun san cewa yara ba sa yin abin da muke fada, suna yin abin da muke yi ne. Idan kuna son:
* Yaran ku su rika faɗin gaskiya, Kada su ji kuna karya a waya ko kuma a zahiri.
* Yaran ku su kasance masu hakuri, Kada su ga kuna yawan fushi da hargagi a gida ko a waje.
* idan kuna son yaron ku su rika girmama mutane, dole ne su ga yadda kuke girmama junan ku da kuma sauran jama'a.
Tarbiyya tana farawa ne ta yadda iyaye s**a gyara kan su. Idan Madubin iyaye ya kasance mai tsafta, hoton da zai nuna wa yaro shi ma zai kasance mai kyau.
Yanzu lokacin nazari ne. Kun taɓa ganin ɗanku ko ɗiyarku suna yin wani hali da kuka san daga gare ku s**a koya?
Ku faɗa mana gaskiya domin baku shawarar data dace.
14/04/2026
Ga masu tambayar ina zasu samu Milk thistle.
Kafin na baku bayanin ina zaku samu milk thistle, ina so ku fahimci wani abu.
Abu na farko da nake so ku fahimta shi ne.
Akwai wani sinadarin dake cikin milk thistle da ake kira silymarin, wannan silymarin din shi ne yake da tasiri sosai gurin taimakawa hanta ta samu waraka.
Shiyasa wasu suke sarrafa milk thistle domin fitar da silymarin din da kyau yadda ake bukata sai su maida shi capsule.
Mafi sauki inda zaku iya samun milk thistle capsule shi ne a online k**ar Jumia ko kuna Konga. Idan mutum bai iya siyayya online ba ya samu wanda ya iya kusa da shi yayi masa.
Abubuwan da mutum zai duba kafin ya sayi milk thistle online. Ku tabbatar da kun duba wadannan bayanan:
1. Dole ku tabbatar da kunga an rubuta (Standardized to 70%–80% silymarin), Idan babu hakan kada ku siya.
2. Ya kasan ce akwai NAFDAC registration number.
3. Dole ku duba expiring date.
4. Kuyi kokarin duba comment din mutane wadanda su ka siya maganin kuga me suke cewa akai.
Capsule yana da ɗan tsada. Zai iya kai ₦15,000 har zuwa ₦30,000 na maganin wata daya. Kuma ana so mutum ya sha maganin na tsawon wata daya ko wata biyu ko wata uku, ya danganta daga girman matsalar ta mutum.
Idan kuma milk thistle seed za'ayi aiki dashi, ana iya samun 1kg din ƴaƴan milk thistle kusan farashin ₦30,000, sai dai kuma 1kg zai iya yima mutun wata uku ko fiye.
Amma kuma mutum zai iya siyan kwatan 1kg ko rabin 1kg ko kuma 1kg ya fara da shi. Iya kudin ka iya shagalin ka
Ana iya samun ƴaƴa milk thistle daga gurin Malam Anas, ga mai bukata sai ya tuntube shi ta number: 08062099966.
Ba dole bane sai kayi amfani da capsule ba idan baka da dama, Seed din ma idan kayi amfani dashi akan tsari mai kyau (k**ar yadda nayi bayani a Hepat**is part 3) zai wadatar.
Allah ya kare mu da lafiya ga baki daya. 🙏🙏🙏
Alhamdulillah I'm back. Ina muka tsaya? Me kuke neman karin haske akai?
Karku damu. Zan baku Numbers din masu saida milk thistle
06/04/2026
🌿 PART 3: 💥 Hantar ka tana neman taimako… amma kai baka sani ba 😢 Ka tsaya ka karanta wannan rubutun kafin cutar ta tsananta! 🌿
To ‘yan uwa, mun iso inda kowa ke jira.
A rubutun baya, mun nuna muku irin barnar da Hepat**is ke yiwa hanta a hankali… amma a yau zan nuna muku yadda zaku taimakawa hantar ku ta fara gyaran kanta cikin hikima da tsari.
👉 Gaskiya daya ce:
Hanta tana da wani abun al'ajabi na ikon warkar da kanta... amma idan ka bata dama ta hanyar aikata wasu tsare tsare, ku biyo ni kuji yadda tsarin yake.
1. MATAKI NA FARKO: FARA YIN GWAJI
Kafin ka fara komai: Ya zama dole ne ka je asibiti ayi maka gwaji domin tabbatar da cutar da kuma yaya yanayin ta yake k**ar yadda mukayi bayanin ire iren gwaje-gwajen da mutum zai iya yi a part 2
MATAKI NA BIYU: DOLE NE A DAKATAR DA DUK WANI ABU DA KE KARA LALATA HANTA
Idan kana son gyara, dole ka tsaida duk wasu hanyoyin dake kara kawo barna. Abubuwan da za'a gujewa su ne k**ar haka:
a. Shan magungunan asibiti ko na gargajiya barkatai ba tare da shawarar masana lafiya ba
b. Zuƙur hayaƙi, shan giya da kuma miyagun kwayoyi
c. Rashin Motsa Jiki
d. Rashin Samun Isashshen Bacci
e. Rashin Samun Hasken Rana da safe (vitamin D)
👉 Ka tuna da cewa: duk abin da ka sha ko ka ci , hanta ce ke wahala da shi domin taga ta tace shi yadda duk wani sinadari mara kyau daga abinda ka ci ko ka sha bazai cutar da dukkan jiki ba.
MATAKI NA UKU: BAWA HANTA HUTU
Kamar yadda nake ta fada muku, duk abincin da kaci hanta ce zata yi aikin tashe shi.
Idan kana cin abinci kowane lokaci (akai akai) babu tsari, yaushe hantar ka zata samu hutun da zata samar da sababbin ƙwayoyin halitta (cell regeneration) domin samun warakar?
Hanta tana kokarin gyara kanta idan ya zama ba'a daura mata aikin tace abinci ba musamman lokacin da mutum yake bacci.
Shi yasa ake son kayi kokarin cin abincin dare da wuri kuma mara nauyi saboda kada abincin yayi mata wahalar tacewa da narkarwa.
A naso kaci abincin dare da wuri, k**ar karfe 8:00pm na dare, daga nan kayi hakuri da cin komai sai dai zaka iya shan ruwa har zuwa washegari karfe 10:00am na safe.
Hakan zai bawa hanta awanni 14 tana hutawa kuma hakan na iya taimaka mata yayin kokarin samar da sababin ƙwayoyin halitta domin gyara kanta.
Sannan kayi kokarin samun isasshen barci na awanni 7-8 da daddare, Domin lokacin barci jiki yana samun damar gyara kansa, kuma hakan yana taimakawa hanta ta yi aikin ta cikin sauƙi.
MATAKI NA HUDU: ABINCIN KA MAGANIN KA
👉 Wannan shine rabin maganin ka. Dole ne mutun ya hakura da wasu abubuwan abincin da ya saba ci yayin da yake kan treatment:
Dole ne mutum ya guji abinci mai dauke da waɗannan abubuwa:
1. Abin mai dauke da Sugar da yawa k**ar:
a. Lemun kwalba da na gwangwani (Sodas/Soft drinks k**ar Coke, Fanta, Pepsi).
b. Alawa, cakulan (chocolates), shayi mai yawan sugar, juice din ƴaƴan itace da aka sawa sugar da kuma madara mai yawan s**ari (Condensed milk).
c. A rage cin farin burodi, cakes, biscuits da dai sauran su, saboda suna saurin komawa s**ari a jiki.
2. A rage yawan nau'ukan maggi da gishiri k**ar yadda aka saba a baya cikin binci. Yin hakan yana jawo kumburi da taruwar ruwa a jiki.
3. Abincin da aka sarrafa shi (Processed Foods): Dole akiyaye amfani da abincin kayan gwangwani ko abincin leda.
4. Nama mai nauyi ko mai yawan kitse k**ar Jan nama mai kitse, Fatar shanu (ponmo), corned beef, sausages da mak**antanta su.
👉 Yana ƙara kumburi a hanta kuma yana hana ta samun sauki yadda ya dace.
5. Soyayyen Abinci k**ar: Soyayyen nama, Soyayyen kifi, ƙosai(Akara), dankali soyayye da chips. Hakan yana ƙara mai a hanta kuma yana jawo matsalar fatty liver.
6. Abinci Mara Tsafta k**ar: Abincin t**i mara tsafta, Kayan marmari da ba a wanke ba, Danyen kifi ko nama da ba'a wanke yadda ya dace ba. Hakan na iya kara karfin cuta ga jiki.
Yanzu kuma abubuwan da ya dace ce mai cutar Hepat**is ya ci a matsayin abinci da zai taimakawa hanta shine:
1. Sinadarin Protein
Hanta tana buƙatar protein domin gyara kwayoyin halittarta da s**a lalace, amma dole ya zama nau'in da ba shi da nauyin narkewa k**ar:
* Kifi (Fish): Musamman kifin da ke da kitse mai kyau (Omega-3) k**ar kifin salla ko wasu kifi na ruwa. Omega-3 yana rage kumburin hanta.
* Farin Naman Kaza (Skinless Poultry): Naman kazar da aka cire wa fata, domin fatar tana da maiko mai yawa.
* Wake da Kwayoyin Shuka (Legumes): Wake, waken suya, da kwayoyin lentils. Sunadarin Plant Protein ya fi sauƙin narkewa a hanta fiye da sunadarin naman saniya.
2. Abincin Hatsi Mai Bawo (Complex Carbohydrates): Wadannan hatsi suna fitar da kuzari (energy) a hankali ne, don haka ba sa ba wa hanta wahala wajen sarrafa s**ari. Misali:
* Shinkafar Gida (Brown/Local Rice): Ba a cire mata dukkan sinadaran cikinta ba, tana da amfani fiye da farar shinkafa.
* Oats: Yana da kyau sosai ga karin kumallo (breakfast) domin yana da sauƙin narkewa.
* Gero da Dawa (Millet & Sorghum): Wadannan sune "Superfoods" na gida. Suna da Fiber mai yawa wanda ke wanke datti.
3. Ganyayyaki da Kayan Lambu (Liver-Cleansing Vegetables)
Wannan shi ne babban sashin "maganin" hanta a cikin abinci, k**ar:
* Kabeji da Broccoli (Cruciferous Veggies): Suna ɗauke da sinadarin Sulfur wanda hanta ke amfani da shi wajen wanke guba (Phase II Detox).
* Shuwaka (Bitter Leaf): Duk da ɗacinta, tana da matukar amfani wajen motsa ruwan daci (bile) wanda ke wanke hanta.
* Alayyahu da Sauran Ganyayyaki: Suna ɗauke da Chlorophyll wanda ke tace gubar jini.
* Karas da Beetroot: Suna da sinadarin Beta-carotene wanda ke ƙarfafa aikin hanta.
4. Itatuwa (Healing Fruits)
* Lemun Tsami (Lemon/Lime): Shan sa a cikin ruwan dumi kowace safiya yana taimakawa hanta yin abinda ya dace.
* Gwanda (Papaya): Tana ɗauke da sinadarin Papain wanda ke taimakawa wajen narkar da abinci da rage nauyin hanta.
* Kankana (Watermelon): Tana taimakawa koda (kidneys) wajen tace ruwa, wanda hakan ke rage wa hanta aiki.
5. Man Da Ya Kamata A Yi Amfani Da Shi (Healthy Fats)
* Man Zaitun (Olive Oil): Wannan shi ne sarkin mai a fannin lafiyar hanta. Yana taimakawa wajen rage kitsen hanta.
* Paya (Avocado): Tana ɗauke da sinadarin Glutathione, wanda shi ne babban antioxidant da hanta ke amfani da shi wajen yaƙi da kwayar cuta.
Wani abin lura game da sarrafa abinci ga mai dauke da Hepat**is shine! Ko da abincin da zaka yana da yana da kyau, idan ka soya shi da mai mai yawa ko wanda bai dace ba, ya na iya zama guba.
Dan haka hanyar da za tafi kyau ita ce hanyar dafawa (Boiling), Gasawa (Grilling/Baking), ko Turara (Steaming).
Wannan tsarin zai sa hantar mutum ta fara samun "sarari" (breathing space) don ta fara yaƙi da kwayar cutar Hepat**is B ko C da kanta.
Nasan a yanayin halin da jama'ar mu take ciki na talauci 😭, ba kowa bane zai iya samun da amfani da wasu daga cikin kayan da ya dace ba.
Hikimar da zakayi wa abincin da Allah ya azurta ka dashi shine kayi kokari amfani da vegetables. masu sauƙin samu su fi abincin yawa k**ar (zogale, lettuce, cabbage tomatoes da albasa). Allah ya kara yassare muna 🙏
Misalin tsarin Abincin da mai hepat**is zai iyayi a yini (Misali ne kawai, kowa sai ya duba dai dai da zarafin da allah yayi masa )
Da safe: Ruwan lemon awa daya kafin cin abinci. Idan za'a karya kuma za'a iya amfani Oats ko kunun gero ko fruit
Da rana kuma Brown rice + ganye + kifi/kaza idan da hali. Idan babu hali karka damar da kan ka. Kayi abinda Allah ya h**e maka.
Da yamma kuma 'Ya'yan itatuwa
Da dare kuma abinci mai sauƙin narkewa (misali wake ko miya mai ganye).
Karku manta da daddare ba'a so a ci abinci mai nauyi saboda kar kaba hanta wahala gurin narkar da abinci mai nauyi.
NOTE: Dole a kula da shan ruwa mai tsafta yadda ya dace k**ar 2-3 litters of water a yini.
MATAKI NA BIYAR :NATURAL MAGUNGUNAN DA ZAMUYI AIKI DASU.
A nan ne mutane da yawa su ke kuskure sai suyi ta shan magunguna barkatai wai don a samu saurin waraka.
Yin tsari mai kyau shi yafi da cewa. Abunda zamuyi amfani dashi ne:
1. 🌿 Milk Thistle. Wannan shi ne sarki kuma ginshikin kula da hanta, yana dauke da wani sinadari dake taimakawa hanta sosai da gaske da ake kira silymarin.
a. Yana kare hanta da daga cutar tayi mata lahani
b. Yana rage kumburin da ya k**a hanta
c. Yana taimakawa sabbin cells su samu
Idan capsule zaka siya, dole ka duba silymarin percent din a jikin kwalbar, idan kuma online ne ka duba percent din a gurin description. Ana bukatar 70% to 80% silymarin.
Yadda zaka sha maganin: idan capsule ne aka samu mai 100mg, za'a sha capsules 3 a yini (safe, rana da kuma dare) bayan cin kowa ne abinci.
Idan kuma mai 150mg aka samu za'a sha sau 2 a rana (safe de yama).
Idan kuma raw seed Milk Thistle mutum ya samu. za'ayi amfani dashi 2 teaspoons (10g) a rana.
👉 Yadda za'ayi amfani da shi:
* Za'a dauki ƴaƴan milk thistle sai a daka ko a markada (very important).
* Sai a raba garin sau gida biyu, ayi amfani da rabi da safe bayan cin abinci sauran rabin kuma da dare bayan cin abin shima.
* Za'a sanya shi cikin koko (pap) ko nono (yoghurt) ko kuma a barbada shi cikin abinci ko miya
Raw seed na milk thistle zai iya karfin aiki k**ar na capsule kuma za'a iya samu akasin haka, saboda ba a san yawan silymarin din da ke cikin sa ba.
2. 🌿 Turmeric + black pepper
Wannan hadin yana rage kumburi kuma yana taimakawa tsaftar hanta
Yadda zaka sha: rabin karamin cokalin turmeric (half teaspoon) + pinch of black pepper sai a hada da ruwan dumi (sau 1 a rana).
⚠️ MUHIMMAN GARGADI
a. Idan kana shan wasu magunguna daban, yana da kyau a samu tazarar 2 hours tsakani.
b. Kada ka wuce kima: shan magani fiye da kima ba yana nufin saurin waraka (zai iya kawo tashin ciki ko gudawa).
c. Masu ciki, masu gallbladder problem, ko masu allergynsu nemi shawarar likita kafin amfani.
⚠️ Disclaimer
Wannan bayani na ilimi ne kawai. Ba ya maye gurbin shawarar likita ko gwaji. Idan kana da cutar Hepat**is ko kana shan wasu magunguna, yana da muhimmanci ka tuntubi likita kafin amfani da wannan tsarin.
**isAwareness
04/04/2026
Karku bari a barku a baya.
ME YA SA YARO YAKE ƘIN JIN MAGANAR IYAYEN SA? 🤔
Ka taɓa kiran yaron ka... ya yi k**ar bai ji ka ba? Ko ka yi masa magana... ya yi kunnen-uwar-shegu?
Iyaye da yawa suna cikin damuwa. Muna ganin yadda yaran da muke so suke kara yin nisa da mu. Rashin kunya, taurin kai, shaye-shaye da abubuwan da muke gudu a waje, yanzu sun dawo cikin gidajen mu.
Tarbiyya tana farawa ne daga Zaman Lafiyar Gida.
Wannan shi ne dalilin da ya sa muka kafa: Elaaj Sirrin Tarbiyya domin sanin:
✅ Yadda za ka sa yaro ya girmama ka don Kauna, ba don Tsoro ba.
✅ Sirrin zaman lafiya a aure (wanda shi ne tushen tarbiyya).
✅ Yadda za ka gyara kuskuren da ka riga ka yi wa yaronka.
Ku kasance tare damu ta hanyar following din Elaaj Sirrin Tarbiyya.
03/04/2026
Na fitar da Hepat**is formulas guda 3 ne. Ina ta kokarin samar muku da hanyar da zatayi muku saukin samun kayan ne sannan nayi posting din.
Nayi hakan ne saboda best formula din, daya daga cikin kayan haɗin ta yana dan da wahala, shiyasa nake kokarin sauƙaƙa muku hanyar samun kayan.
Alhamdulillah yanzu na kai karshen wasu ɓangarorin, yanzu saura ɓangare daya. In sha Allah zuwa gobe komai ze kai karshe, daga nan sai na sakar muku da post din. Allah yasa haka yafi zama alkhari.
02/04/2026
Na kammala tsara muku cikakken bayani na ƙarshe akan Hepat**is (Part 3), kuma zan wallafa shi gobe In shaa Allah.
A halin yanzu, ina kan tattaunawa da wasu daga cikin masu siyar da kayan magungunan daga wurare daban-daban domin na bincika ingancin su, amincin su da kuma nema muku sauƙin samun kayan kafin na haɗa ku da su.
Kamar yadda kuka sani manufata ita ce:
✔️ ku fara samun ilimin cutar
✔️ ku fahimci jikin ku yadda ya dace
✔️ sannan ku yanke shawara mai kyau
Gobe zaku samu cikakken bayani mai zurfi, mai tsari, kuma wanda zai taimaka muku wacen korar cutar in shaa Allah.
Ku danna follow and share domin kasancewa tare da Elaaj sirrin lafiya a koda yaushe.
**isAwareness
Magani ba alewa bane.
01/04/2026
🤔 MAGANI BA ALEWA BA NE: YA KAMATA KU SAN MEKE DAMUN KU KAFIN KU SHA MAGANI.
Na lura da yadda mutane da yawa suke neman a basu magani akan ciwon dake damun su ba tare da sun samu tabbacin matsalar su ba.
Na san kuna son samun sauƙi da wuri, amma akwai babban dalili da ya sa na ke series program. Ina yin hakan ne domin jama'a su samu ilimin matsalolin su kafin shan magani. Hakan za taimaka sosai gurin samu warakar matsalar ku.
Me ya sa hakan keda muhimmanci?
Saboda bada kariya ga lafiyar Hanta da Koda: Shan magani ba tare da an tabbatar da abin da yake damun ka ba, babban haɗari ne.
Idan ka sha maganin da bai dace ba, maimakon ka warke, kana iya janyo wa kanka ciwon hanta ko koda.
Me ya sa bana posting kullum?
Ina yin hakan ne don:
* In samu lokacin duba sakonnin ku (DMs): Ranar da ban yi posting ba, ita ce ranar da nake amsa tambayoyinku daki-daki.
* Ba ku damar karantawa: Ina so ku samu lokacin nutsuwa ku fahimci darasin da na bayar, ba wai kawai ku duba ku wuce ba.
Lafiya tafi kudi, kuma ba a gaggawa a cikinta. Idan har ka gane cewa kariya ta fi magani, kuma kana tare da mu a wannan tsarin: Ku rubuta "MUNA TARE" a comment. 👇
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Sokoto
