Abdullahi Sambo

Abdullahi Sambo

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abdullahi Sambo, Health/Beauty, Dandinmahe, Sokoto.

25/03/2026

Nasara daga Allah

ayau membobin Kungiyar Gyara kayanka youth foundation Dandin-mahe (Hisbah) sunyi Zama na musamman domin Kara inganta ayyukansu tareda fitowo da sabbin tsare-tsare

Acikin zaman Wannan Kungiya Mai albarka sunyi bita akan shawarwarinda s**a samu daga jami'an tsaro da shugabannin gari da malaman addini

Daga karshe Wannan Kungiya tayi addu'a zuwaga mutanen kirki wadanda sukewa wannan Kungiya fatan alkhairi

Bayan kammala wannan zaman membobin Wannan Kungiya sun zagaya wajen aiki (operation) domin tabbatarda tarbiyya da bin doka da oda da taimakawa wajen samarda tsaro domin taimakawa jami'an tsaro

Allah ya taimake gaskiya ya rusa karya da makaryata a Duk inda suke

15/02/2026

Yana daga cikin alamun imani kauna saboda Allah da kiyayya saboda Allah duk Wanda Zaka soshi to ka tabbata Don Allah Zaka soshi hakama idan Zaka kishi to ka kishi saboda Allah

A yanzu danake magana bansan abinda gobe zata haifarba Amma Ina fatan alkhairi acikin zuciyata inason inga mutum Mai kishin addini Mai son kawo Gyara Mai fada da barna koda bansan inda yafitoba Kuma idan Dan siyasa ne zangoyi bayansa ako wace jam'iyya yake

Haka zalika inajin bacin rai ga Wanda yazama kishiyar haka koka gida daya muke jini daya, inason inyi amfani da wannan damar inyi Kira zuwaga yan uwana musamman matasa mu canza tunanimmu na neman biyan bukatummu kawai batareda Sanya manufar addinimmu gaba ba

Idan zakayi yabo ko zagi kafin kayi kafara tunani shin maslahar addini ce tasa Zan yabe wane ko in sokeshi kokodai bukatatace kawai yan uwa mu tuna cewa babu wani Abu da Zaka samu ko yasameka face an rubuta haka tun kafin kazo duniya

Annabi S.a.w Yana cewa

ان روح القدس نفث في روعي انه لن تموت نفس حتى تستكمل رزقها واجلها فاتقوا الله واجملوا في الطلب ولا يحملن احدكم استبطاء الرزق ان تطلبوه بمعصية الله فانما عند الله لا ينال بمعصيته

Ma'ana"Hakika Ruhi Mai tealki(Mala'ika jibrilu) ya saukarda wahayi zuwagareni cewa babu wata rayuwa dazata mutu har Sai ta kammala canye arzikinta da kuma ajalinta saboda haka kuji tsoron Allah kubi hanya Mai kyau wajen nema kada jinkirin zuwan arziki yasa kunemeshi ta hanyar sabon Allah domin abinda ke wajen Allah ba'a samunsa ta hanyar sabamasa"

Wannan tunatarwace daga Dan uwanku
Abdullahi Sambo Dandin-mahe

Allah yasa mugane.

16/12/2025

Alhamdulillah amadadin kungiyar gyara kayanka youths Foundation Dandinmahe (Hisba) suna mika godiya ta musamman zuwaga Hukumar yan sanda dake garin Dandinmahe akan wani samame da hukumar ta kai jiya cikin dare a dakunan mata masu zaman kansu (Karuwwai) inda ake aikata alfasha suna laka gidan sauro ga fili suna kwana da maza inda jami'an yan sanda da yan vegilenty(yan banga) s**a fatattaki wadannan mabarnata.

Ko shakka babu wannan abin ayabane kuma cigabane mai alfanu gameda sha'anin tarbiyya da wannan ne muke yabawa shugabanninmu da malumanmu da kuma wannan hukumar ta yan sanda da yan vegilenty kuma wannan wani karfafawane ga aikin da kungiyar Hisba keyi agarin Dandinmahe ta kewaye Dafatar Allah ya shirye mu zuwaga tafarki madaidaici.

Sako da kungiyar gyara kayanka youths Foundation Dandinmahe (Hisba)
Abdullahi Sambo (Secretary)

29/06/2025

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN A yau Lahadi bayan sallar azzahar Allah ya jarabceni da tashin gobara a dakin iyalina inda gobarar ta lakume kayan daki da littafai masu yawa ina neman addu'a ga Yan uwa Musulmi baki daya

Photos from Abdullahi Sambo's post 22/04/2024

اللهم ارزقنا علما نافعا Allah ka azurtamu da ilimi mai amfani

22/04/2024

Kubada kadan Allah yabaku Mai yawa وما أنفقتم من شيء فهو يخلفه وهو خير الرازقين

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Sokoto?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Dandinmahe
Sokoto